<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>69</hymn_number>
<lyrics>[V1]
 1) Yesu, maganar rai, lura da ni.
 Nan cikin duniya ga zunubi.
 Shaiɗan da wayonsa ya ruɗe ni,
 Zo nan da ikonka, ka cece ni.

[V2]
 2) Yesu, mai fansar rai, ka wanke ni
 Da jinin sadaka mai tsarki.
 Tun da ka ba da rai saboda ni,
 Jawo ni wurinka, ka riƙe ni.

[V3]
 3) Yesu,  gurasar rai, ba ni in ci
 Yadda ka bayar da a Galili.
 Ba ni da kome nan sai kai kaɗai,
 Kullum ka cishe ni da jibin rai.

[V4]
 4) Yesu, mai ba da rai, tuna da ni.
 Alherin halinka ya gamshc ni.
 Zubo da Ruhunka, tsabtad da ni,
 Har zan yi nasara da zunubi.</lyrics>
<title>Yesu, Maganar Rai, Lura da Ni LW69</title>
</song>